Rahotanni daga Sudan na cewa, a yau Litinin ne ake sa ran shugaban kasar Omar al-Bashir, zai kai ziyara a Juba, babban birnin Sudan ta Kudu don ganawa da takwaransa na kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit a kokarin shawo kan tashin hankalin da ke faruwa a kasar.
A makonnin da suka gabata, an yi ta gwabza fada a kasar tsakanin sojojin gwamnati da ke goyon bayan shugaba Kiir da 'yan tawayen da ke marawa tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar baya.
A cewar rahotannin MDD, fadace-fadacen sun haddasa mutuwar mutane sama da 1,000, kana sama da fararen hula 121,600 sun rasa gidajensu, yayin da wasu 63,000 ke samun mafaka a sansanonin MDD da ke sassan kasar.
A baya-bayan nan, kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afirka (IGAD) ta sanar da cewa, an fara wata tattaunawar samar da zaman lafiya a hukumance tsakanin bangarorin biyu a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha. (Ibrahim)