Manzon kasar Sin a MDD, kana shugaban karba-karba na kwamitin sulhu na MDD na wannan karo, Liu Jieyi, ya bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan a aiwatar da jerin yarjejeniyoyin da kasashen Sudan da Sudan ta Kudu suka cimma a tsakaninsu, don a inganta dangantakar da ke tsakanin sassan biyu tare da warware sauran batutuwan da suke takaddama a kai.
Liu Jieyi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, bayan tattaunawar da kwamitin ya gudanar a asirce game da kasashen biyu.
Ya ce, kwamitin mai mambobi 15, yana sa-ido sosai game da batutuwan kasashen na Sudan da Sudan ta Kudu, wanda ya ce, an samu ci gaba sosai a 'yan kwanakin nan.
Manzon na Sin ya ce, shugabannin kasashen biyu, wato Omar Al-Bashir da Salva Kiir Mayardit, sun ziyarci juna tare da cimma matsaya kan wasu batutuwa, ciki har da batun tsallaka kan iyaka, kafa yankin da kasancewar soji da kuma batun mai.
Ya yi gargadin cewa, kamata ya yi kasashen biyu, su aiwatar da yarjejeniyoyin da suka cimma, inda ya ce, duk wani matakin da ko wane bangare zai dauka sabanin yarjejeniyoyin da sassan biyu suka cimma, ba zai haifar da mai ido ba a wannan lokaci.
Bugu da kari, Mr. Liu ya lura da cewa, kasar Sin ta damu game da gazawar da aka yi ta yiwa yara kusan 165,000 allurar rigakafin cutar shan-inna a jihohin kudancin Kordofan da Blue Nile na Sudan da yaki ya wargaza. (Ibrahim)