Sakamakon kuri'ar raba gardama da al'ummar yankin Crimea na kasar Ukraine suka kada, ya nuna cewa, kaso sama da 95 bisa dari na goyon bayan ficewar yankin daga karkashin ikon Ukraine.
Wannan dai sakamako na nuna cewa, al'ummar ta Crimea na da burin komawa karkashin ikon kasar Russia, matakin da ya sanya da dama daga masu goyon bayan Rashan fara bayyana farin cikinsu a kan titunan yankin.
Jagoran masu goyon bayan Rasha a Crimea ya bayyana cewa, zai mika bukatar yankin na komawa bangaren kasar Rasha a Litinin din nan.
Tuni dai shugaba Vladimir Putin na kasar ta Rasha, ya bayyana goyon bayansa ga sakamakon da kuri'ar za ta haifar, duk da kuwa kin amincewa da kungiyar tarayyar Turai, da Amurka suka yi da hakan. Suna masu cewa, kuri'ar raba gardamar haramtacciya ce.
Wani kudurin da Amurka ta gabatar a zauren majalissar tsaro ta MDD, na haramta wannan kuri'a ya hadu cikas, bayan da Rasha ta hau kujerar ta ki. A kuma Litinin din nan ne ake sa ran ministocin kasashe mambobin kungiyar EU, za su tattauna batun yiwuwar kakabawa Rashan takunkumi. (Saminu)