Shugaba Barack Obama na Amurka, ya yi watsi da batun kuri'ar raba gardama kan makomar yankin nan na Crimea, yana mai gargadin Rasha da ta kaucewa keta dokokin kasa da kasa kan batun makomar yankin.
Shugaban na Amurka ya bayyana hakan ne ga manema labaru a jiya Laraba, bayan kammala ganawarsa da firaministan kasar Ukraine Arseniy Yatsenyuk a fadar White House.
Obama ya kuma ce, kasarsa, da gamayyar kasashen duniya za su dauki tsattsauran mataki kan Rasha, muddin ta kuskura ta yi kutse ga wani yanki na kasar Ukraine. Daga nan sai ya bayyana cikakken goyon bayan sa ga gwamnatin kasar ta Ukraine mai helkwata a birnin Kiev.
Sai dai a daya bangaren kuma, mahukuntan kasar Rasha sun ce, a shirye suke, su goyi bayan duk wata matsaya da al'ummar yankin Crimea suka zaba, bayan kammala kuri'ar raba gardama da za su kada.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai 'yan majalissar dokokin Crimean, suka kada kuri'ar neman amincewa da komawar yankin karkashin ikon kasar Rasha, matakin da zai baiwa al'ummar yankin damar kada kuri'a kan hakan a ranar Lahadi mai zuwa. Haka za lika a ranar Talatar da ta gabata kuma, majalissar ta amince da kudurin samun 'yancin kai, da zarar al'ummar yankin sun amince da komawa bangaren karkashin ikon kasar ta Rasha. (Saminu)