Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei, ya ce, Sin na da burin tabbatar da adalci da daidaito, don gane da halin da kasar Ukraine ta fada, tana kuma fatan masu ruwa da tsaki kan lamarin za su rungumi hanyar maslaha, domin warware takaddamar da ke faruwa.
Wannan dai tsokaci na Mr. Hong, ya biyo bayan fitar sakamakon kuri'ar raba gardama ce, da al'ummar yankin Crimea suka kada a ranar Lahadi.
Bugu da kari Hong ya ce, kasar Sin ta damu kwarai da yadda lamari ke kasancewa a kasar ta Ukraine, tana kuma fatan dukkanin bangarorin da batun ya shafa za su kai zuciya nesa, su kuma gaggauta hawa teburin shawara, domin warware matsalar ta hanyar siyasa da martaba juna. (Saminu)