in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta kawo shawarar da za'a bi a warware matsalar Ukraine
2014-03-11 16:30:01 cri

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov a ranar Litinin din nan ya ce, kasarsa ta kawo shawarar da za'a bi a shawo kan matsalar da ta kunno kai a kasar Ukraine bisa tsarin dokoki, sai dai kuma kasashen yammaci suna barazanar garkamawa Rasha takunkumi.

A cikin shawarar, za'a duba halin da ake cikin a Ukraine din bisa dokar kasa da kasa, sannan a yi la'akari da dukkan bukatun kasar, in ji Mr. Lavrov a lokacin da yake yi wa shugaban kasar Rashan Vladimir Putin bayani a birnin Sochi.

Wannan shawara ta Rasha ta zo ne bayan da Amurka ita kuma ta kawo tata shawarar a kan Ukraine din ranar Juma'ar da ta gabata, wadda Rashan ba ta gamsu da ita ba, in ji Lavrov.

Sai dai duk da shawarar da Rashan ta gabatar, kasashen yammaci suna kara azama a kan kasar ta hanyar barazanar kakaba mata takunkumi, baya ga sanar da dakatar da ba da takardun iznin shiga kasashensu, da kuma kulle duk wata ajiya ta kudi da kaddarorin wassu daga cikin 'yan kasashen na Rasha da Ukraine dake kasashensu tun daga Alhamis din da ta gabata.

Yanzu haka 'yan majalissar dattawar kasar ta Amurka suna shirin rattaba hannu a kan dokar za ta kara matsin lamaba a kan takunkumin da aka saka wa Rasha da zai hada da hana ba da taimakon jin kai, in ji wani 'dan majalaissar dattawan Amurkan a jiya Litinin. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China