Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi da takwaran shi na kasar Poland, Radoslaw Sikorski, sun tattauna ta wayar tarho a game da halin da ake ciki a kasar Ukraine.
Ministan harkokin wajen, ya ce, kasar Sin tana goyon bayan kokarin da kasashen duniya ke yi na samar da zaman lafiya tare da fatan, nan ba da jimawa ba, za'a cimma wata yarjejeniyar siyasa, wacce za ta tabbatar da 'yancin dukanin kungiyoyin kabilu na Ukraine, tare da kaucewa tashin hankula da kuma samar da zaman lafiyar mai dorewa a yankin.
A nashi bangaren, ministan harkokin waje na Poland Sikorski ya ce, Poland za ta ci gaba da tuntubar kasar Sin a kokarin da ake na magance rikicin a siyasance. (Suwaiba)