Shugaba Barack Obama na Amurka, ya sake yin kira ga Rasha da ta dauki matakan diflomasiyya, wajen warware takaddamar siyasar kasar Ukraine. A daidai gabar da takwaransa na Rashan Vladimir Putin ke cewa, kasarsa na bin dokokin kasa da kasa sau da kafa don gane da batun.
Shugabannin biyu sun bayyanawa juna ra'ayoyin nasu ne, yayin wata tattaunawa da suka yi ta wayar tarho a jiya Alhamis. Yayin wannan tattaunawa, Obama ya bayyanawa Putin cewa, matakan da Rasha ke dauka a Crimea, sun sabawa dokokin dake kare ikon kasar Ukraine. Wanda kuma hakan ya sanya ala tilas Amurkan, ta fara daukar wasu matakai kamar sauran takwarorinta na kasashen Turai.
Shugaba Obama ya ce, kamata ya yi Rasha ta shiga tattaunawa da mahukuntan Ukraine, akwai kuma bukatar tura jami'an sa ido na kasa da kasa, domin tabbatar da kare hakkokin fararen hula a Ukraine.
Har ila yau shugaban na Amurka, ya shawarci sojojin Rasha da su koma sansaninsu na asali dake Crimea, kuma Rashan ta goyi bayan babban zaben shugaba kasa da za a gudanar a Ukraine cikin watan Mayun dake tafe.
Shi kuwa a nasa bangare, shugaba Putin, cewa ya yi, gwamnatin kasar ta Ukraine mai ci haramtacciya ce, wadda kuma ta dare mulki ta hanyar juyin mulki, tana kuma zartas da haramtattun kudurori ga yankunan gabashi da na kudu maso gabashin kasar, da ma yankin Crimea.
Don haka, a cewarsa, Rasha ke daukar matakan daidaita wannan batu bisa dogaro da dokokin da suka tabbata tsakaninta da kasar ta Ukraine. (Saminu)