Firaministan kasar Somaliya Abdiweli Sheikh Ahmed Mohamed ya sha alwashin kawar da mayakan Al-Shabaab daga dukkan sassan kasar ya zuwa karshen shekarar 2014.
Mohamed ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na hadin gwiwa da mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto ranar Talata a Nairobi, babban kasar Kenya, inda ya ce, har yanzu akwai wasu muhimman sassan kasar da ke karkashin ikon 'yan tawayen ba wai baki dayan shiyyar ba.
Kungiyar ta Al-Shabaab, ta lashi takwabin kai jerin hare-hare a kasar, musamman kan jami'an tsaro da ke aiki a garuruwan da ke kan iyakar arewacin Kenya, inda ta halaka mutane da dama a wasu hare-haren da ta kai da nakiyoyi da gurneti.
A watan Nuwamban da ya gabata ne, kasar Kenya ta kutsa kai zuwa iyakar Somaliya da nufin farautar mayakan na Al-Shabaab da ake zargi da kai jerin hare-haren gurneti da nakiyoyi da aka binne a karkashin kasa a Nairobi, Mombasa da kuma yankin arewacin kasar.
Sama da 'yan Somaliya miliyan 1 ne suka ketara zuwa kasar Kenya sakamakon matsalar tsaro.
Mataimakin shugaban Kenya William Ruto ya bukaci gwamnatin kasar ta Somaliya da ta yi kokarin samar da kayayyakin more rayuwa a yankunan da aka kwace daga hannun 'yan tawayen, ta yadda 'yan gudun hijirar da suka dawo za su ji dadin zama. (Ibrahim)