Rahotanni daga Mogadishu na nuna cewa, a kalla maharan kungiyar Al-Shabaab 8 ne suka hallaka, wassu 5 kuma suka jikkata bayan da wata mota mai dauke da bam ta tarwatse ba zato a garin Bulo Burte dake tsakiyar kasar Somaliya, in ji wassu masu gani da ido da kuma jami'an tsaro.
An dai ji karar fashewar mai karfin gaske a Bulo Burte dab da babban garin Beledewyne wanda sojojin gwamnati ke rike da shi cikin hadin gwiwwa da sojojin kungiyar AU.
Sojoji sun bayyana cewa, motar da aka shirya, an yi niyyar kai hari da ita ne a sansanin sojojin gwamnati da na zaman lafiya na AU dake Beledewyne mai tazaran kilomita 300 daga arewacin Mogadishu, babban birnin kasar.
Da yake bayani ta kafar rediyon Mogadishu, mukaddashin kwamnadan soji na yankin Hiran, Mohammed Amin Adam ya ce, kungiyar ta Al-Shabaab ta kara yawan hare-haren da suke kaiwa a kan fararen hula, sannan akwai sauran bayanai da suka samu game da wassu shirye-shiryen kungiyar.
Mohammed Amin Adam ya yi bayanin cewa, a wannan lokacin, suna da cikakken bayani game da wata motar daukan mai makare da ababen fashewa da ke kan hanyarta zuwa Beledweyne daga Bulo Burte wadda maharan suka yi jigila.
Wannan dai ya zo ne bayan da aka samu fashewar bama bamai har sau biyu a wurare daban daban a Mogadishu, abin da ya hallaka mutun daya, sannan guda biyar suka jikkata, ciki har da wani jami'in gwamnati wanda ya samu raunin lokacin yake tuka motarsa, kuma bam din da aka dana a jikin motar ta tarwatse a kan titin Makka Al Mukarama na Mogadishu. (Fatimah)