Kwamitin tsaro na MDD a ranar Alhamis din nan ya yi suka da kakkausar murya game da mummunan harin bam din da aka kai cikin wata mota a Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya, yana mai jaddada cewa, yana nan akan bakansa na ganin ya murkushe duk wani nau'in aiki da ya shafi ta'addanci.
A cikin wata sanarwa da aka fitar, an ce, mambobin kwamitin sun nuna matukar damuwarsu game da harin na ranar Alhamis wanda kungiyar Al-Shabaab ta dauki alhakin kaiwa, kuma sun yi suka da babbar murya a kan hakan.
Kwamitin tsaron ya tabbatar da aniyarsa ta cigaba da goyon bayan duk kokarin kasa da kasa wajen tunkarar barazanar ayyukan ta'addancin da wannan kungiyar ta Al-Shabaab ke gudanarwa.
A safiyar wannan ranar ne wani 'dan kunar bakin wake cikin wata mota dauke da bam ya fada shagon saida shayi a Mogadishu, abin da ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 11, kamar yadda rahoto ya nuna, wannan shagon shayin shi ne inda manyan jam'an leken asiri na yawan zuwa wajen.
Kungiyar Al-Shabaab mai alaka da Al-Qaida wadda ta dauki alhakin kai harin, yanzu haka ta kara yawan hare-haren da ta kan kai a babban birnin kasar. (Fatimah)