in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ukraine tana da damar kulla abota da kasashen yammaci da Rasha, in ji Obama
2014-03-05 10:24:02 cri

Shugaba Obama na kasar Amurka ya ce, kasar Ukraine tana da damar kulla abota da kasashen yammaci da kuma Rasha, muddin dukkan sassan ba za su kasance a cikin kasar tare da tsoma baki cikin harkokinta na cikin gida ba.

Obama ya yi wadannan kalamai ne, a matsayin mayar da martani kan yadda kasar Rasha ta mamaye yankin Crimea, bayan da aka tumbuke Viktor Yanukovych da ke goyon bayan shugaban Rasha a ranar 22 ga watan Fabrairu, kana ya tsallaka zuwa kasar ta Rasha, bayan da aka kwashe kusan watanni 3 ana bore a kasar.

Amurka ta zargi Rasha ta tura dubban sojoji zuwa Crimea, matakin da ya harzuka kasar ta Amurka dakatar da duk wata huldar soja da tattaunawar cinikayya da Rasha, sannan ta sanar da baiwa Ukraine rancen dala biliyan 1.

Sai dai shugaba Putin ya gargadi Amurka da sauran kasashen da ke ikirarin kargama mata takunkumi da cewa, kaikayi ne zai koma kan mashekiya. Ya kuma bayyana abin da ke faruwa a Ukraine a matsayin juyin mulkin da ya saba wa doka.

Putin ya ce, har yanzu Yanukovichy ne halattacen shugaban kasar Ukraine, ko da ya ke ba shi da iko a hannunsa. Sai dai mambobin majalisar zartaswar kasar ta Ukraine sun fara tattaunawa da takwarorinsu na kasar Rasha da nufin kashe wutar rikicin da ke ruruwa tsakanin kasashen da ke makwabtaka da juna. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China