in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci Isra'ila da Palesdinu da su yi kokarin ganin an samu wani cigaba
2014-03-10 10:16:20 cri

Manzon musamman na kasar Sin da yanzu haka yake ziyara a yankin Gabas ta Tsakiya Wu Sike a jiya Lahadi ya bukaci Palesdinu da Isra'ila da su yi kokari wajen ganin an samu wani cigaba a tattaunawar zaman lafiya da ake yi.

Bayan ganawar da ya yi da shugaban al'ummar Palesdinu Mahmoud Abbas, Mr. Wu ya shaida wa Xinhua cewar, kasar Sin ta damu matuka game da cikas din da ake samu a kan tattaunawar zaman lafiya a yankin, ya ce, Sin tana ganin ya kamata dukkanin bangarorin biyu su yi iyakacin kokarin su na ganin an samu cigaba.

Mr. Wu ya kuma ce, kasar Sin za ta cigaba da ba da taimakonta ga cigaban tattalin arzikin kasar Palesdinawa, ciki har da horas da kwararru, ba da kwarin gwiwwa ga ma'aikatun kasar Sin su shiga ayyukan raya kasar, da samar da ababen more rayuwa, da kuma inganta harkar makamashi.

A wani labarin kuma, a wata sanarwa da aka fitar bayan ganawarsa da manzon na kasar Sin, firaministan Palesdinu Rami al-Hamdallah ya yi kira ga kasar Sin da ta ba da kwarin gwiwwa ga kamfanonin kasar su nemi iznin da za su samu damar ayyukan hako man fetur a yankunan Palesdinu. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China