Babban kwamitin zartarwa na kungiyar neman 'yancin Palesdinu LPO ya yanke shawara a ranar Litinin da yamma domin gabatar da takardar shiga MDD domin mai da martani kan gine-ginen mazagunan Yahudawa.
Bayan wani zaman taron da shugaban Palesdinawa Mahmoud Abbas ya jagoranta a birnin Ramallah, kungiyar LPO ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, kwamitin siyasarta na sauke nauyin shirya wani shirin neman shiga MDD nan take.
Wannan mataki na da manufar sake maido da matakin da MDD ta dauka game da amince da kasar Palesdinu a matsayin mai sa ido a MDD, da kuma amince da shiga kudurori, yarjejeniyoyi da kungiyoyi na MDD, in ji wannan sanarwa.
Kwamitin zartaswa na LPO, wato babbar hukumar siyasa ta Palesdinawa, ya bayyana cewa, ja da bayan da ake samu kan zaman lafiya a Palestinu na da nasaba da matsayi da matakan da gwamnatin Isra'ila ta dauka, masamman ma kan cigaba da gina mazugunan Yahudawa, wannnan abun kunya ne, kuma gwamnatin Isra'ila na cigaba da yin haka domin maida hannun agogo baya ga shirin wanzar da zaman lafiya da kuma kokarin mamaye Jerusalem da yammacin gabar kogin Jordan, in ji sanarwar LPO. (Maman Ada)