Jirgin samfurin B777-200 ya taso ne daga Kuala Lampur ne babban birnin kasar Malaysia da misalin karfe 12.41 da safiyar asabar din nan kuma ana sa ran zai sauka Beijing da misalin karfe 6.30 na safiyar yau din a bayanin da kamfanin jiragen saman Malaysia ta bayar.
Hukumar kula da zirga zirgan jiragen saman na Sin ta tabbatar da cewa jirgin mai lambar MH370 yana dauke da Fasinjoji 227 da suka hada da ma'aikatan jirgin 12 da Sinawa 154.
Shi ma Ministan harkokin kasashen wajen Sin Wang Yi a safiyar asabar din nan ya bayyana cewa kasar ta damu matuka game da kasa tuntubar wannan jirgi. (Fatimah Jibril)