Mr. Li ya gabatar da wannan kira ne, yayin wata tattaunawa a yau din nan, da takwaransa na kasar ta Malesiyan Najib Razak ta wayar tarho.
A wani ci gaban kuma, hukumar lura da harkokin tekun kasar Sin, ta bayyana cewa, yanzu haka dakarun tsaron gabar tekun kasar sun bazama, zuwa sassan tekun da ake tsammanin jirgin fasinjan nan na kasar Malesiya ya fadi. A shirin su na ceton rayukan mutanen da jirgin ke dauke da su.
Koda yake kawo yanzu ba a tabbatar da inda wannan jirgi ya fadi ba, a hannu guda akwai rade-radin cewa jirgin ya fada wani yankin tekun kasar Vietnam ko Malesiya.
An dai daina jin duriyar wannan jirgi ne, sa'o'i kadan bayan da ya bar filin jirgin Kula Lumfur na kasar Malesiya, a hanyar sa ta zuwa nan birnin Beijing da sanyin safiyar Asabar din nan.(Saminu Alhassan)