Babbar jam'iyyar adawa ta Renamo da ke kasar Mozambique, ta koka kan hare-haren da dakarun gwamnati ke kai musu a tsakiyar kasar, yayin da sassan biyu ke bayyana kudurinsu a farkon wannan mako na tsagaida bude wuta.
Kakakin jagaron Renamo, Antonio Muchanga, ya bayyana cewa, jam'iyyarsa ta yi mamakin yadda dakarun gwamnatin dauke da muggan makamai suka durfafi sansanin jam'iyyar a daren ranar Talata.
Sai dai kakakin tawagar gwamnatin Frelimo Jose Pacheco, a tattaunawar da suka yi da Renamo, ya mayar da martanin cewa, dakarun gwamnatin suna farautar wadanda ake zargi da kai hare-hare ne kan motar soja a ranar Litinin, harin da ake zargin Renamon da kaiwa.
A daya bangaren kuma, tawagogin biyu sun bayyana kudurinsu na kawo karshen fadace-fadacen da suka faru a ranar Litinin bayan zaman sasantawar.
Pacheco ya tabbatar da cewa, an samar da matakan samar da zaman lafiya, ko da yake ba yanzu za a bayyana su ba.(Ibrahim)