Shugaba Armando Guebuza na kasar Mozambique, ya yi kira ga 'yan adawar kasar da su ajiye makamansu, bayan shafe kusan wata guda ana bata-kashi tsakanin dakarun gwamnatin kasar da na 'yan adawar.
Guebuza ya ce, lokaci ya yi da kungiyar Renamo za ta amsa kira, ta ajiye makamai, domin rungumar hanyoyin sulhu da za su kai ga shiga tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.
Yayin da yake amsa tambayoyin da aka yi masa cikin wani shiri na gidan talabijin, shugaba Guebuza ya jaddada cewa, tattaunawa ce kadai za ta iya warware yanayin da ake ciki a halin yanzu. Ya ce, yana fatan ba da jimawa ba, za a kai ga hawa teburin shawara tsakaninsa da jagoran kungiyar ta Renamo Afonso Dhlakama.
Bangarorin biyu dai sun fara fafatawa ne tun a ranar 21 ga watan Octobar da ya gabata, bayan da dakarun 'yan tawayen Renamo, suka yiwa jami'an tsaron gwamnati kwantan-bauna a Satunjira, dake yankin Gorongosa, a tsakiyar lardin Sofala.
Aukuwar hakan ke da wuya sai dakarun gwamnatin suka farma garin na Satunjira, maboyar shugaban kungiyar 'yan tawayen ta Renamo.
Lamarin da ya tilasa Dhlakama tserewa tare da wasu dakaru dake tare da shi.
Daga bisani shugaba Guebuza ya bukace shi da ya halartar wani zaman tattaunawa a Maputo a ranar 8 ga watan Nuwambar nan, sai dai hakan ya ci tura, ko da dai ba a ma tabbatar ko gayyatar da aka yi masa, ta isa gare shi ba ko kuwa a'a. (Saminu)