in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jagoran 'yan tawayen Mozambique na samun mafaka a wani boyayyen wuri
2013-11-26 10:34:35 cri

Babban sakataren jam'iyyar Renamo ta 'yan adawar kasar Mozambique Manuel Bissopo, ya bayyana wa manema labaru cewa, har ya zuwa yanzu, jagoran jam'iyyar tasu Afonso Dhlakama, na ci gaba da samun mafaka a wani boyayyen wuri da bai bayyana shi ba. Ya kuma ce, Dhlakama, na da burin bayyana nan ba da jimawa ba.

Yayin da yake karin haske kan yunkurin kame Dhlakama da sojoji suka yi a Satunjira dake lardin Sofala, Bissopo ya ce, suna tare a maboyar jagoran nasu, lokacin da sojojin suka yi wa garin na Satunjira tsinke. Ya kuma tabbatar da cewa, har ya zuwa yanzu jagoran nasu bai fice daga kasar ba.

Babban sakataren jam'iyyar ta Renamo, ya kuma kara da cewa, shugaban nasu, ba zai amince ya amsa gayyatar da shugaba Armando Guebuza ya yi masa ba, har sai an tabbatar da ba shi kariyar da ta dace.

Har ila yau, Renamon na bukatar a janye dukkanin sojojin da ke ci gaba da sintiri a sassan yankin Satunjira, a kuma baiwa masu sa ido daga ketare damar halartar tattaunawar da bangarorin biyu ke yi. Sai dai mahukuntan kasar sun ki amincewa da shigar masu da ido daga ketare, suna masu cewa, za su iya ba da damar sanya ido ne kawai ga masu ruwa da tsaki na cikin gida. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China