in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun gwamnatin Mozambique sun kara kai samame kan maboyar 'yan tawayen Renamo
2013-10-30 10:48:22 cri

A ranar Talata ne sojojin gwamnatin kasar Mozambique, suka yi dirar mikiya kan maboyar babbar jam'iyyar adawar kasar Renamo a lardin Nampula.

Zaman dar-dar din da ke tsakanin sassan biyu a cikin 'yan shekarun nan, yana haifar da babbar barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar da ke kudancin Afirka.

Sojojin sun bayyana cewa, 'yan tawayen na Renamo sun kaddamar da hari kan 'yan sandan kwantar da tarzoma da ke yankin, kana suka arce zuwa wani wurin da ba a sani ba.

Sassan biyu sun shafe kusan sa'a guda suna musayar wuta, lamarin da ya sanya mazauna yankin barin gidajensu.

A wani labarin kuma, a ranar Talata, sojojin sun kwace sansanin 'yan tawayen da ke Maringue da kuma Sofala, inda gidan talabijin na kasar Mozambique din ya nuno hotunan bukkokin da 'yan tawayen suka gudu suka bari, makamai, kujeru da tebura da sauran kayayyaki.

Bayanai na nuna cewa, ana ci gaba da fuskantar zaman zullumi a tsakiyar gundumomin Maringue da Muxungue, inda rahotanni ke cewa, a watan Mayun shekarar da muke ciki, an gwabza fada a yankin Muxungue har aka hallaka 'yan sandan kwantar da tarzoma da 'yan tawayen Renamo, lokacin da sojoji ke yiwa motoci rakiya domin su ratsa ta yankin.

Tun a shekarar da ta gabata ce dai, Renamo da kuma gwamnatin kasar wadda jam'iyyar Frelimo ke jagoranta suke zaman 'yan-marina.

Jagoran Renamo Afonso Dhlakama, ya yi barazanar kauracewa zaben kananan hukumomin da aka shirya gudanar a watan Nuwamba, kana ya ce, ba za a gudanar zabukan da aka shirya gudanarwa a watan Oktoban shekara mai zuwa ba, har sai an gyara dokokin zaben kasar na yanzu.

Idan ba a manta ba, a ranar Litinin ne, Renamon ta fice daga tattaunawa da gwamnati da nufin sasanta rigingimun siyasa da kasar ta kwashe shekaru biyu tana fuskanta. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China