Babbar jami'ar hukuma mai kula da 'yan gudun hijira ta MDD a tarayyar Najeriya, Angele Dikongue-Atangana, ta ce, akwai kimanin 'yan Najeriya 17,000 da yanzu haka ke neman mafaka a kasashen dake makwaftaka da kasar.
Dikongue-Atangana, wadda ta bayyana hakan jiya a Abuja, babban birnin tarayyar kasar, ta ce, wannan adadi, na kunshe da 'yan kasar dake gudun hijira a kasashen Chadi, da Kamaru da Nijar, sakamakon rigingimun dake addabar arewa amso gabashin kasar.
A cewar jami'ar, hukumar lura da 'yan gudun hijiyar ta MDD ko UNHCR, na hadin gwiwa da wadannan kasashe, domin tabbatar da kare hakkokin 'yan gudun hijirar. Dikongue-Atangana, ta kara da cewa, matsalar tsaro ce ke kan gaba, cikin manyan kalubalen dake addabar dubban al'ummun dake duniya, matakin da ya sanya a yanzu haka, duniyar ke fuskantar matsalar yawaitar 'yan gudun hijira, da ta haura wadda aka taba samu cikin shekaru 20 da suka gabata
Jami'ar ta kuma alakanta halin matsi da al'ummun wasu kasashen gabashin Afirka ke ciki, da matsalolin tsaro, da rashin ayyukan yi, da kuma fari. (Saminu)