Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) ta bayyana cewa, a kalla 'yan kasar Sudan ta Kudu 14,800 ne suka tsallaka zuwa kasar Kenya sakamakon fadan da jaririyar kasar ke fama da shi.
A wani rahoton da babbar kwamishinar hukumar ta bayar, ya nuna cewa, wasu 'yan kasar ta Sudan ta Kudu 242 sun isa kan iyakar Nadapal a ranar Laraba, ko da ya ke hukumar ta ce, adadin wadanda ke yin kaurar ya ragu.
Fadan ya barke ne lokacin da aka samu tsamin dangantakar siyasa tsakanin dakarun shugaba Salva Kiir da na tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar a watan Disamba, inda aka yi imanin cewa, dubban jama'a sun halaka yayin da kimanin mutane 900,000 suka bar gidajensu, baya ga karin wasu 123,000 da suka arce zuwa kasashe makwabta.
A watan jiya ne dukkan bangarorin biyu suka sanya hannu kan yarjejejniyar tsagaita bude wuta bisa shiga tsakanin kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afirka (IGAD) a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha. An kuma shirya gudanar da zagayen tattauna na gaba da za a yi a kasar ta Habasha a ranar 10 ga watan Fabrairu, inda kungiyar ta IGAD ta gayyaci sassan da ke fada da juna, ciki har da fursunonin siyasar da aka saki da su halarta.
A cewar MDD, kimanin kashi 80 cikin 100 na 'yan gudun hijirar kasar Sudan ta Kudu da ke sansanin 'yan gudun hijirar Kakuma, matasa ne, kana kashi 13 cikin 100 mata ne da dattawa, yayin da kashi 7 cikin 100 maza ne tsoffi. (Ibrahim)