Manzon musamman ta ofishin kula da 'yan gudun hijira na MDD UNHCR, kuma shahararriyar 'yar wasan kwaikwayon nan Angelina Jolie a ranar Litinin din nan ta yi kiran da a dakatar da tashin hankalin da ake yi a Sham bayan da ta ziyarci wassu sansanonin 'yan gudun hijira ta kasar dake zaune a kasar Lebanon.
A cikin wata sanarwa da ofishin kula da 'yan gudun hijirar ta fitar, an ce, Jolie ta tattauna da firaministan kasar Lebanon Tamman Salam, a inda ta yi nuni a kan karamci da goyon bayan da kasar da al'ummarta ke baiwa makwabtansu.
Angelina Jolie a ziyararta ta uku a Lebanon a madadin majalissar domin ta ga halin da yara kanana 'yan kasar Sham din ke ciki, ganin cewar yanzu tashin hankalin ya shiga shekara ta hudu.
Ta yi maraba da kudurin da majalissar ta yanke na ba da taimakon jin kai ga kasar ta Sham wanda ta ce, abu ne da ya kamata a yi da dadewa, wanda zai taimaka wa dubban al'ummar kasar maza, mata da yara kanana da ba su ci ba ba su sha ba, da wannan tashin hankali ya rutsa da su. (Fatimah)