Kakakin hukumar UNHCR Fatoumata Lejeune-Kaba ta bayyana a gun taron manema labaru a wannan rana cewa, bisa binciken da hukumomin MDD ciki har da hukumarta suka yi a jihohi 9 na kasar Afirka ta Tsakiya a watanni biyu da suka gabata, an ce, kashi 99 cikin dari na kananan yara dubu 168 ba su ci gaba da yin karatu bayan barkewar yakin, kana an tilasta kashi daya cikin kashi biyar na yawan yaran da suka bar makaranta da shiga kungiyoyin dakaru. Kashi 88 cikin dari na mutanen kasar da aka bincika sun bayyana halin jin tsoro da damuwa a zuciyarsu. A sakamakon rikice-rikicen da suka faru a kasar, yawancin jama'ar kasar ba su iya samun abinci, kana akwai hadarin sace abincin da suke da shi. Don haka, hukumar UNHCR ta yi kira ga sojojin gwamnatin kasar da kawancen dakaru masu adawa da su tabbatar da tsaron jama'ar kasar da nuna goyon baya ga hukumomin MDD da suke bada gudummawar jin kai a kasar.
Madam Lejeune-Kaba ta kara da cewa, ban da ma rikice-rikicen kasar Afirka ta Tsakiya da suka kawo illa ga tsaron jama'ar kasar, sun kuma kawo cikas ga gudanar da ayyukan bada ceto da hukumomin jin kai na MDD suke yi a kasar. Hukumar UNHCR ta dawo da wasu ma'aikatanta zuwa birnin Bangui, babban birnin kasar Afirka ta Tsakiya. (Zainab)