in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta sa ido sosai game da cinikin hauren giwa.
2013-11-08 16:39:36 cri
A 'yan kwanan baya, mataimakin direkta a ofishin kula da safarar dabbobi, ko itatuwan dake daf da bacewa daga doron kasa na kasar Sin Meng Xianlin, ya bayyana cewa a ko da yaushe kasar Sin na mai da hankali matuka ga batun kiyaye giwaye, tare da daukar tsauraren matakan sa ido, game da sana'ar sayar da hauren giwa.

A cewar wannan jami'i, ko da a shekarar bana ma sai da hukumar 'yan sanda da ke kiyaye daji ta kasar Sin, ta shigar da kararraki kimanin 60, wadanda suka shafi cinikin hauren giwa, bayan ta kame hauren giwayen da nauyinsa ya kai kilogram sama da dubu 1.

Meng Xianlin ya kara da cewa, a shekaru da dama da suka gabata, kasar Sin ta tashi tsaye wajen yin hadin gwiwa da kasashen waje, don tabbatar da kiyaye rayuwar giwaye. Domin ci gaba da kiyaye rayuwar tasu, kasar Sin ta kafa asusun kiyaye giwaye na kasa da kasa, inda a ko wace shekara, take marawa kasashen Afrika da dama baya, da sauran kungiyoyin kasa da kasa wajen kiyaye giwaye. Haka zalika Sin na bada kudaden domin gudanar wannan aiki daga asusun na kiyaye giwaye.

Bugu da kari, Sin na goyon bayan ayyukan yaki da fasakwaurin hauren giwaye, kuma ta shirya taron nazarin kasa da kasa, domin yaki da ciniki, da fasa kwaurin hauren na giwaye, tare da shirya taron kara-wa-juna-sani game da kiyaye rayuwar giwaye, inda ta gayyaci jami'an kasashen da ke da giwaye daga kasashen nahiyar Afrika.

Bisa labarin da aka samu, an ce, bisa kokokin kasar Sin, an ba da umurnin yin hukunci ga masu sana'ar shige da ficen hauren giwaye ba bisa ka'ida ba, kana kuma an yankewa masu laifuka dake da alaka da hakan da dama, hukuncin daurin watanni 6 zuwa daurin rai da rai.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China