A ran 6 ga wata MDD ta yaba wa kasar Sin kan matakin da ta dauka na lalata hauren giwa a fili karo na farko, MDD ta ce wannan lamarin yana da ma'anar ishara.
Hukumar da ke kula da harkokin gandun daji ta kasar Sin, da babbar hukumar kwastan ta kasar sun gudanar da aikin lalata hauren giwa a birnin Dongguan na lardin Guangdong da ke kudancin Sin, inda suka lalata hauren giwa da nauyinsu ya kai ton 6.1, wadanda hukumomin biyu suka kama.
Mataimakin babban sakataren MDD, kuma darektan zartaswa na hukumar tsara shirin muhalli ta MDD Mista Achim Steiner ya taya murna musamman ga kasar Sin, tare da amince da kokarin da hukumar da ke kula da harkokin gamdun daji ta kasar Sin take yi wajen lalata hakoran giwa.
Mista Achim Steiner ya ce, giwaye suna fuskantar barazana mai tsanani a cikin shekaru fiye da goma da suka gabata, amma hadin kai a tsakanin kasashen duniya ya riga ya share fage ga rage bukatun hakoran giwa da kara aiwatar da dokokin domin kare giwaye. Sin da Amurka da dai sauransu kasashen duniya sun samu ci gaba matuka wajen lalata hauren giwa.
Babban sakataren hukumar kare namun daji da ke fuskantar barazanar bacewa wato CITES Mista John E. Scanlon ya yi nuni cewa, wannan aikin lalata hauren giwaye da Sin ta gudanar ya bayar da wani abun yabo ne ga kasar da ma duniya cewa, Sin ba ta yarda da cinikin hauren giwa ba bisa doka ba. Ya kara da cewa, hadin kai a tsakanin kasa da kasa zai taimakwa wajen aiwatar da dokoki yadda ya kamata da rage bukatun hauren giwa, kasashen duniya suna da niyyar kawo karshen cinikin hauren giwa ba bisa doka ba.(Danladi)