in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya yi allahwadai da hare-haren da aka kai a Iraki
2014-02-07 10:34:22 cri

Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon, ya yi allahwadai da jerin hare-haren baya-bayan nan da aka kai a sassan kasar Iraki, ciki har da ma'aikatar harkokin wajen kasar, wadanda suka yi sanadiyar jikkatar mutane da dama.

Ban Ki-moon ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa ta hannun kakakinsa, yana mai kira ga 'yan kasar ta Iraki, da su hada kansu don tunkarar ayyukan ta'addanci. Ya ce, MDD tana goyon bayan gwamnati da al'ummar kasar Iraki a wannan kokari, ya kuma mika ta'aziyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

Alkaluma na nuna cewa, mutane 48 ne suka mutu yayin da wasu 119 suka jikkata a hare-haren na ranar Laraba da safe, lokacin da wani bam da aka nada a cikin wata karamar mota ya tashi a wajen ginin ma'aikatar harkokin wajen kasar da ke tsakiyar birnin Bagadaza daura da wasu ofisoshin gwamnati da na jakadancin Amurka.

Sai dai har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wadannan munanan hare-hare inda bayanan ofishin MDD da ke gudanar da ayyuka a kasar ta Iraki suka nuna cewa, 'yan Iraki 8,869, ciki har da fararen hula da 'yan sanda 7,818 ne aka kashe a shekarar 2013, adadi mafi yawa a cikin shekarun da suka gabata. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China