Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya yi kashedi a ranar Alhamis kan kara tabarbarewar tsaro a kasar Iraki wanda ke iyar sanya kasar cikin wani yakin basasa, da tsunduma kasar cikin zaman dar dar, ganin yadda tashe-tashen hankali suke kara tsananta cikin wannan kasa dake makwabtaka da kasar Syria da ita ma take cikin rikici
Kasar Iraki na cikin wani hali na tsaka mai wuya dalilin tashen-tashen hankali dake cigaba da bazuwa a wasu kasashen wannan shiyya, in ji mista Kerry a wata hirarsa da manema labarai bayan ya gana da takwaransa na kasar Iraki Hoshyar Zebari.
Masu kishin islama 'yan Sunni da 'yan Shi'a na gaba da junansu a cikin wannan shiyya, lamarin da ka iyar kawo barazana ga zaman lafiyar kasar Iraki, in ji mista Kerry.
Munanan hare-hare dake cigaba da abkuwa a kasar Iraki da tawagar ba da agajin jin kai ta MDD a kasar Iraki ta fitar a cikin wani rohoton ya bayyana cewa, 'yan kasar Iraki dubu daya suka mutu a hare-haren ta'addanci da tashe-tashen hankali a cikin watan Juli, wanda ya kasance wani mafi muni fiye da shekaru biyar da suka gabata.
Hakazalika, mista Kerry ya bayyana munanan ayyukan keta hakkin bil'adama da kungiyar Al-Qaida ta aiwatar tare da hare-haren ranar Lahadi wadanda suka hadasa mutuwar mutane 74 a yayin bikin karamar sallah da ta kawo karshen watan Ramadan.
A nasa bangare, mista Zebari ya jaddada cewa, kasarsa ba za ta fada ba cikin yakin basasa, kuma na addini. Jami'in diplomasiyyar kasar Iraki ya bayyana cewa, ya zo Washington domin neman taimakon kasar Amurka da kuma wata dangantaka ta fuskar tsaro. (Maman Ada)