in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 19 sun mutu a wassu hare-hare a Iraki
2014-02-10 10:27:29 cri

Rahotanni na nuwa cewa, a kalla mutane 19 ne suka mutu sakamakon hare-hare da dama, wadansu kuma suka jikkata a sassa daban daban na kasar Iraki, kamar yadda mahukuntar 'yan sandan kasar suka tabbatar.

Wani jami'in 'yan sanda da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa Xinhua cewa, a jiya Lahadi 9 ga wata, mutane biyu sun mutu, guda 7 suka jikkata lokacin da wata motar dauke da bam ta fashe kusa da kasuwa a garin Sadr na mabiya darikar shi'a dake gabashin Bagadaza.

Haka kuma wata mota dauke da bam ta kai hari ga sojoji masu yawon sintiri a garin Mahmoudiyah mai tazaran kilomita 30 daga kudancin Bagadaza, babban birnin kasar inda soja daya ya mutu, masu tafiya a kusa da wajen su uku suka jikkata.

Har ila yau, a wannan rana a gabashin gundumar Diyala, fararen hula 3 sun hallaka, ciki har da yaro karami, sannan da sanyin safiyar ranar kuma mutane 5 suka jikkata lokacin da wassu bama bamai guda uku da aka dana a gefen titi suka tarwatse a unguwar al-Gatoon dake kudu maso yammacin gundumar Baquba.

Ban da haka, 'yan sanda sun gano gawawwakin mutane biyu da aka harba a kai, sannan a jefa su a rafi kusa a kudancin Baquba, in ji majiyar 'yan sanda kuma a wannan yankin har ila yau, wassu 'yan bindiga sun bude wuta a motar wani jami'in 'yan adawa na darikar shi'a Asa'ib Ahl al-Haq da shi da dogarinsa, abin da ya sa ya samu rauni dogarinsa kuma ya mutu. Wannan majiyar 'yan sanda ya shaida wa Xinhua cewa, an harbe wassu 'yan sanda 6 da 'yan adawa da al'Qaida su 4 a wurare daban daban a gundumar Salahudin.

A daren ranar Asabar, 'yan sanda sun gano gawar wani da kungiyar Sahwa da gwamnati ke marawa baya da yaransa uku wadanda wassu 'yan bindiga suka sace su kwanaki uku da suka gabata a gidansu kusa da garin Tikrit dake arewacin Bagadaza.

Iraki dai ta dade tana fuskantar tashin hankali, bisa kididdigar ofishin ba da agajin MDD, an ce, a kalla mutane 8,868 suka hallaka a shekarar da ta gabata kawai, abin da ya haura adadin sauran shekarun baya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China