Akalla mutane 17 suka mutu yayin wasu 57 suka jikkata a jerin hare-haren bom da aka adana kan motoci a ranar Lahadi a Bagadaza, babban birnin kasar Iraki, a wani labarin da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu daga wata mijiyar 'yan sandan kasar.
Hari mafi muni ya abku a ranar Lahadi da yamma yayin da wasu motoci makare da boma bomai suka fashe a wata kasuwar unguwar Shaab dake arewa maso gabashin Bagadaza, tare da kashe mutane 9 da raunana 28, a cewar wannan majiya.
Haka kuma majiyar ta cigaba da cewa, wata bam ta tashi a cikin wata mota a kusa da kasuwar dake unguwar Jamila a gabashin Bagadaza, tare da kashe mutune 4 da raunana 12.
Harin na hudu ya faru a wata mahadar al-Khillani dake tsakiyar birnin Bagadaza tare da halaka mutum guda da jikkita mutane 5, a cewar majiyar 'yan sandan.
Wasu boma bomai sun tashe a yankunan kasuwanci na Maidan da Souq al-Arabi dake cike da jama'a a tsakiyar Bagadaza wadanda suka halaka mutane 3, tare da jikkata wasu 12.
Wadannan hare-hare sun faru a lokacin da jami'an tsaron kasar Iraki da na kabilun Sunni ke fafatawa tare da mayakan kungiyar Al-Qaida a cikin biranen jihar Anbar dake yammacin kasar. (Maman Ada)