Amurka ta jaddada goyon bayanta ga hukumomin Najeriya wajen binciken abin da ta kira ayyukan da matsora ke nunawa na ta'addanci domin gurfanar da masu aikata hakan a gaban kuliya, in ji sakataren harkokin wajenta John Kerry
A cewar Mr. Kerry, al'ummar arewacin Najeriya su cancanci su samu kwanciyar hankali su daina faragaban duk wani tashin hankali, don haka Amurka za ta ba da taimakonta wajen dakile wadannan ayyukan ta'addanci tare da taimaka wa hukumomin kasar fidda wani tsari nagartacce domin fuskantar barazanar da kungiyar nan ta Boko Haram ke haifarwa tare da kare al'ummar da tabbatar da 'yancinsu na dan adam
Babban jami'in kasar Amurkan ya ce, kasarsa ta kasance mai goyon bayan Najeriya a har kullum wajen kokarinta na ganin ta murkushe kungiyar nan ta Boko Haram da duk wassu kungiyoyi masu alaka da irin haka.
A ranar 15 ga wata ne dai wassu 'yan bindiga suka kai farmaki, inda suka hallaka mutane sama da 100 a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, da yanzu haka ya zama cibiyar kungiyar nan ta Boko Haram, sannan kwanaki kadan da wannan suka sake kai wani harin da ya hallaka wassu mutane da dama, wassu kuma suka jikkata. (Fatimah)