in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya zai gana da shugaban Amurka a wata mai zuwa
2013-08-15 09:43:56 cri

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan zai gana da shugaban kasar Amurka Barack Obama a birnin Washington a yayin babban taron MDD da za'a yi a watan Satumba a birnin New York, a cewar wata jami'ar kasar Amurka, ranar Laraba a Abuja.

Karamar sakataren harkokin siyasa ta kasar Amurka Wendy Sherman ta baiyana hakan ne ga manema labarai jim kadan bayan wata ganawa ta sirri da ta yi da shugaba Jonathan.

Sherman wacce ita ce ta jagoranci ganawa ta hukumar hadin gwiwa tsakanin kasar Amurka da Najeriya, wanda za'a fara yau Alhamis, ta ce, ta mika wasika ne ga shugaban Najeriya daga takwaransa na kasar Amurka.

Jami'ar kasar Amurkan ta jadadda irin muhimmiyar rawa da Najeriya ke takawa a cikin kungiyar bunkasa tattalin arzikin yankin Afirka ta yamma (ECOWAS), da ayyukan kiyaye zaman lafiya a duk fadin duniya.

Ta ci gaba da cewa, hukumar hadin gwiwa tsakanin Amurka da Najeriya wata muhimmiyar kafa ce ta yin aiki tare, tsakanin kasashen biyu domin inganta dangantakarsu.

Sherman ta ce, hukumar za ta baiwa Najeriya goyon baya a yayin da take kara jan damarar fuskantar kalubale dake gabanta.

Ta baiyana wa manema labarai cewa, batutuwa dake gaban hukumar sun kunshi harkokin tsaro, shugabanci, ba da ilmi da kuma harkar noma. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China