A Nigeriya, gwamnonin jihohin arewacin kasar a ranar Lahadin nan suka bukaci gwamnatin tarayya da ta kara yawan jami'an tsaro da suke da kayayyakin aiki fiye da na wadanda ake da su yanzu a jihohin da ke fuskantar tashin hankali.
Gwamnan jihar Niger kuma shugaban gwamnonin arewacin kasar Babangida Aliyu ya bukaci hakan a cikin wata sanarwa da kakakinsa Danladi Ndayeko ya raba wa manema labarai.
Gwamna Babangida Aliyu ya ba da misali da mutane 13 da wassu 'yan bindiga suka hallaka a jihar Filato da ke tsakiyar kasar a ranar Asabar din da ta gabata, abin da ya sa ya bukaci sojoji da su sake duba dabarun shawo kan wannan lamari domin kare lafiyar jama'a da 'yan kungiyar Boko Haram ke kashewa kullum.
Ya yi bayanin cewa, daukacin gwamnonin jihohin arewa sun amince a lokacin taron da suka yi a Kaduna da su dauki matakai a kan barazanar yanayin tsaro da makiyaya ke haifar wa yankin, don haka suke bukatar gwamnatin tarayya da ta samar da wani tsari na kasa baki daya da zai sasanta makiyaya da sauran jama'a ta hanyar fitar masu da burtali da kuma inda dabbobinsu za su yi kiwo.
Taron gwamnonin arewan ya kuma yi roki na musamman ga gwamnatin tarayya da ta samar da isassun kudade ga jihohin da wannan tashin hankali ya shafa domin rage asarar da suke fuskanta. (Fatimah)