Kakakin majalissar wakilai a Nigeriya Aminu Tambuwal a ranar Lahadin nan 23 ga wata ya karyata rahotannin dake cewa, ya taba yin niyyar canza sheka zuwa jam'iyyar adawa ta APC.
Aminu Tambuwal ya karyata hakan ne jim kadan bayan fitowa daga wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasar Nigeriya Olusegun Obasanjo a gidansa da ke jihar Ogun da ke kudu maso yammacin kasar.
Alhaji Tambuwal wanda ya jaddada cikakken halarcinsa na 'dan jam'iyyar PDP ya shaida wa manema labarai cewa, ya je gidan Obasanjon ne domin ziyarar ban girma ga dattijon kasa, sannan kuma ya tattauna da shi game da wassu al'amurra da suka shafi kasa.
Kakakin majalissar wakilan ya ce, Obasanjo shugaba ne ba kawai a kasar ba, har ma a Afrika, kuma ya dace ga su dake rike da mukaman iko da shugabanci su rika kawo ziyara jifa jifa domin neman shawarar shi a kan al'amurra da suka shafi kasa, a don haka ne ya kai wannan ziyara.
Ganin cewa babban zabe na shekara ta 2015 ya karato jam'iyyar dake mulki PDP, a yanzu haka ta rasa gwamnonin jihohi 5 da kuma 'yan majalissar wakilai da na dokoki da dama ga jam'iyyar adawa ta APC, wadda ita ce mafi girma a cikin sauran jam'iyyun adawa. (Fatimah)