in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fuskantar matsalar karancin ruwa a arewacin Afirka, in ji FAO
2014-02-21 10:26:33 cri

Hukumar samar da abinci da aikin gona MDD (FAO) ta yi gargadin cewa, daya daga cikin babbar matsalar da ke barazana ga batun samar da abinci a kasashen gabashi da arewacin Afirka ita ce matsalar ruwa, inda aka yi kiyasin cewa, ruwan da yankin ke samu zai ragu da kashi 50 cikin 100 ya zuwa shekarar 2050.

Gargadin da hukumar ta yi, ya zo ne yayin da ministocin da jami'an aikin gona ke shirin daukar matakai yayin wata ganawa da ofishin shiyya na hukumar zai fara a ranar Litinin mai zuwa, inda za su tattauna batun sabon shirin magance matsalar ruwa da shiyyar ke fuskanta, wadda hukumar ta FAO ta kaddamar da nufin taimakawa kasashen mambobin hukumar wajen bullo da manufofi da dabarun magance matsalar karancin ruwa da kuma matsalolin da suka shafi abinci.

Mataimakin darektan hukumar, kana wakilin kasashen gabashi da arewacin Afirka na hukumar Abdelssalam Ould Ahmed, ya ce, shiyyar ta taka rawar gani cikin shekaru 20 da suka gabata a bangaren amfani da ruwa da hanyoyin tattara shi, amma har yanzu akwai sauran rina a kaba muddin ana bukatar a inganta bukatar samar da ruwa a bangaren aikin gona, kare ingancin ruwa, magance kalubalen da ke shafar matsalar canjin yanayi.

Wannan shi ne taron hukumar FAO karo na 32 na shiyyar gabashi da arewacin Afirka da aka shirya game da magance matsalar ruwa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China