in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar FAO za ta kara kokarin samar da abinci a Somalia
2014-01-20 10:41:55 cri

Hukumar samar da abinci da aikin gona ta MDD (FAO) ta bayyana cewa, za ta kashe kimanin dala miliyan 120 a wannan shekara wajen kara samar da abinci a kasar Somalia.

Wakilin hukumar da ke kasar ta Somalia Luca Alinovi ne ya bayyana hakan ranar Asabar, lokacin da ya ke zantawa da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua yayin taron zuba jari a kasar, yana mai cewa, za a yi amfani da kudaden ne wajen taimakawa bangaren kiwon dabbobi, kamun kifi da aikin gona a kasar da ke kusurwar Afirka, ta yadda za a magance sake abkuwar yunwar da ta abkawa kasar.

Taron na yini guda, ya samu halartar sassa masu zaman kansu, gwamnati, jami'an bayar da agaji da za su sanya ido kan damar da sassan masu zamansu ke da ita a kasar ta Somalia, ganin cewa, kasar tana da albarkatun dabbobi mafi girma a Afirka, duk da shekarun da aka kwashe, ana tashin hankali a kasar.

Ya ce, Allah ya albarkaci kasar Somaliya da albarkatun ruwa, amma ba a kyakkyawan amfani da kifafen da ta ke da su, sakamakon shekarun da aka kwashe, ana fama da tashin hankali da ayyukan 'yan fashin teku a kasar, sannan kuma al'ummar kasar ba su damu da cin kifi ba.

Bayanai na nuna cewa, fari da kuma tashin hankalin da ake fama da su a kasar, sun sanya hukumomin agaji ba sa iya gudanar da ayyukansu yadda ya kamata tare da kaiwa ga mutanen da ke kudancin kasar.

Sai dai karin taimakon agaji gami da amfanin gonan da aka samu a wannan karon, sun taimaka wajen inganta yanayin jin kai a kasar da yanzu haka kusan za a ce ba a jin radadin fari. Amma duk wani abin da zai kawo cikas kan tallafin da ake samu, zai mayar da hannun agogo baya game da nasarorin da aka samu, tun lokacin da aka ayyana yunwa a kasar a watan Yulin shekarar 2011.

Har yanzu dai kasar ta Somalia tana fama da matsalar karancin abinci, sakamakon fari da yunwa da suka abkawa kasar a shekarar 2011, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China