Bisa sakamakon wani binciken da kungiyar noma da cimaka ta majalisar dunkin duniya (FAO) da asusun kasa da kasa kan cigaban noma (FIDA) suka fitar a ranar jiya, an ce, yana da kyau a kara samar da albarkatun noma, kawo goyon baya ga yin takara da kuma samar da dama ga manoma shiga kasuwanni domin baiwa kasashen yammacin Afrika damar bunkasa bangaren nomansu.
Kan taken sake karfafa hanyoyin cimaka na yammacin Afrika, rahoton na gabatar da jerin binciken da aka yi cikin nasara na yawaita zuba jari a yankin cikin hanyoyin bunkasa noma, sakamakon matsalar karancin abinci a duniya a shekarar 2007 zuwa 2008.
Wannan rahoto na nuna cewa, kasashen na iyar samun alfanu sosai bisa taimakon kungiyoyi da hukumomi kan muhimman bangarori da suka shafi cigaban noma daga dukkan fannoni, da kuma samun damar daidaita harkoki tsakanin manoma, masana'antu masu zaman kansu, masana'antun gwamnati da kuma bangaren da hukumomin kudi.
Ko da yake wasu kasashen yammcin Afrika sun fi wasu saura samun cigaba, amma shiyyar na baya idan aka kwatanta ta da wasu yankunan Afrika ta fuskar muhimman gine-gine, zuba jari, bincike, cigaba da kuma sarrafa albarkatun noma, in ji mista Aziz Elbehri, babban masanin tattalin arziki na FAO, daya daga cikin wadanda suka rubuta wannan rahoto.
Haka zalika rahoton na nuna cewa, ya kamata shiyyar ta mai da hankali wajen bunkasa muhimman ayyukan nomanta, da wani lokaci ta yi watsi da su domin mai da hankali kan albarkatun noman da take fitarwa zuwa kasashen waje. (Maman Ada)