in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Ansar Beit Al-Maqdis ta dauki alhakin harin ranar Lahadi a Sinai dake Masar
2014-02-18 10:24:41 cri

Kungiyar masu tsattsauran ra'ayin Islama dake da alaka da Al-Qaida ta Ansar Beit Al-Maqdis, ta ce, ita ce ta kaddamar da harin da aka kaiwa wata motar 'yan yawon shakatawa a kudancin Sinai dake daf da iyakar Masar da Isra'ila a ranar Lahadin da ta gabata.

Maharan kungiyar dai sun tada wani bom ne, wanda ya tarwatsa wata motar safa, dake dauke da 'yan yawon shakatawa, da yawancin su 'yan kasar Koriya ta Kudu ne, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane 4, baya ga wasu da dama da suka jikkata.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta yanar gizo a ranar Litinin, ta ce, 'ya'yan kungiyar za su ci gaba da kaiwa mahukunta, da sassan tattalin arzikin kasar makamantan wadannan hare-hare, a yunkurin da suke yi na tsugunar da kasar. Sanarwar ta kuma bukaci baki 'yan yawon shakatawa da su gaggauta ficewa daga kasar ta Masar nan da kwanaki 4, domin kaucewa aukuwar abin da ya faru a zirin Sinai.

Duk da cewa jami'an tsaron kasar Masar na shan fama da hare-hare daga kungiyoyin 'yan adawa, sakamakon hambarar da gwamnatin shugaba Mohammad Morsi a watan Yulin bara, wannan ne karon farko da aka kaiwa 'yan yawon shakatawa, ko fararen hula farmaki.

Sashin yawon shakatawa dai na sahun gaba, wajen kawowa kasar ta Masar kudaden shiga, kafin ya fara samun koma baya a shekarar 2011, sakamakon hambarar da gwamnatin Hosni Mubarak da kuma ta Mohammad Morsi da sojojin kasar suka yi. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China