Kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta yi matukar yin allahwadai da harin da aka kai kan hedkwatar 'yan sanda a kasar Masar.
A cikin wata sanarwa da shugabar hukumar zartaswar kungiyar Madam Nkosazana Dlamini-Zuma ta bayar a ranar Jumma'a, ta yi matukar yin allahwadai da harin da ta kira na masu tsaro da aka kai kan hedkwatar 'yan sanda a kasar ta Masar, wanda ya yi sanadiyar rayuka tare da jikkatar wasu da dama.
Shugabar kungiyar ta jaddada cewa, wannan harin ya sake nuna bukatar da ke akwai ta kara zage damtse wajen yaki da 'yan ta'adda a nahiyar baki daya, kamar yadda dokokin nahiyar da na kasa da kasa suka tanada. (Ibrahim)