in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya yi allahwadai da harin ta'addancin da aka kai a Masar
2014-02-17 10:50:38 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi allahwadai da kakkausar murya kan harin ta'addanci da aka kai ranar Lahadi kan wata motar bas dauke da masu yawon bude ido a kudancin Sinai na kasar Masar, harin da ya haddasa mutuwar mutane 4, ciki har da direban motar da masu yawon shakatawa 'yan kasar Koriya ta Kudu guda uku yayin da wasu da dama suka jikkata.

Wata sanarwa da Ban Ki-moon ya bayar, ta mika ta'aziyarsa ga gwamnatocin kasashen Masar, Koriya ta Kudu da kuma iyalan wadanda harin ya rutsa da su, sannan ya yi kiran da a hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

Wannan dai shi ne hari na farko da aka kai kan masu yawon shakatawa, tun lokacin da sojoji suka tumbuke mulkin shugaba Mohamed Morsi a watan Yulin shekarar da ta gabata, lamarin da ya haddasa bore da kai hare-hare a sassan kasar, musamman kan jami'an tsaro. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China