in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan Masar sun ayyana kungiyar 'yan uwa musulmi a matsayin kungiyar 'yan ta'adda
2013-12-26 10:14:28 cri

Gwamnatin kasar Masar, ta zargi kungiyar 'yan uwa musulmi ta hambararren shugaba Mohamed Morsi da hannu a harin bam din da aka kai a hedkwatar 'yan sanda da ke Mansoura, tare da ayyana kungiyar a matsayin kungiyar 'yan ta'adda a hukumance.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da gwamnatin kasar ta Masar ta fitar a ranar Laraba, inda a ciki ta ce, dukkan Misirawa sun kadu da wannan danyen aikin da kungiyar ta aikata a ranar Talata, harin da ya tarwatsa hedkwatar 'yan sandan yankin Daqahleya, tare da kashe a kalla mutane 16, kana wasu sama da 130 suka jikkata.

Mataimakin firaministan kasar ta Masar kana ministan ilimi mai zurfi na kasar, Hossam Eissa, ya ayyana cewa, kungiyar ta 'yan uwa musulmi da ke cikin kasar da ma wajen Masar, kungiya ce ta 'yan ta'dda, inda ya zargi su da neman wargaza shirin mika mulki na kasar.

Ya ce, za a yi amfani da dokar ayyukan ta'addanci kan duk wani mutum da aka samu da hannu a wannan danyen aiki, ko daukar nauyin masu aikata shi ko yayata ayyukan kungiyar.

Yanzu dai ana ci gaba da gudanar da bincike kan harin na Mansoura, ko da yake kungiyar masu kishin Islama ta Ansar Beit al-Maqdis da ke a yankin Sinai ta yi ikirarin cewa, ita ta kai harin, a hannun guda kuma kungiyar 'yan uwa musulmi ta yi allahwadai da harin.na ranar Talata. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China