Sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya fara ziyara a kasashen Turai da yankin Gabas ta tsakiya
Tun daga ranar 24 ga wata, sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Forbes Kerry, ya fara ziyarar kasashe 9, cikinsu hadda kasashen Turai da yankin Gabas ta tsakiya, kuma makasudin ziyarar tasa shi ne tattauna batuttuwan kasashen Mali, da Siriya, da kuma Afghanistan. Wannan shi ne karo na farko da Kerry ya kai ziyara a kasashen waje, bayan da ya dare kujerar sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka. Haka kuma, an bayyana cewa, zai shafe kwanaki 11 yana wannan ziyara, inda ake fatan zai ziyarci kasashen Birtaniya, da Jamus, da Faransa, da Italiya, da kuma Turkiyya. Sauran kasashen da zai ziyara sun hada da Masar, da Saudiyya, da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Qatar.(Bako)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku