Wakilin din din din na kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya bayyana cikakken goyon bayan da kasarsa ke baiwa MDD, game da kudurin baiwa fararen hula kariya, a kasashe da yankunan dake fama da rigingimu.
Mr. Liu ya bayyana hakan ne yayin zaman mahawara da kwamitin tsaron majalissar ya gudanar a ranar Laraba 12 ga watan nan. Yace akwai matukar bukatar kara mai da hankali wajen zurfafa tattaunawa domin cimma burin da aka sanya gaba.
Kiu ya kara da cewa, kare rayukan fararen hula yayin tashe-tashen hankula ko yake-yake, aiki ne da ya rataya a wuyan kasashe, ko yankunan da abin ya shafa, baya ga daukacin kasashen duniya da ya wajaba su ba da tasu gudummawa a matakin na gaba.
Don gane da batun baiwa hakkokin bil'adama kariya kuwa, wakilin kasar ta Sin cewa ya yi, ya zama wajibi a baiwa hukumomin shari'a na kasa da kasa cikakken goyon baya, a matsayinsu na masu ruwa da tsaki a wannan fanni.
Bana ne dai aka cika shekaru 15, da zartas da kudurin kwamitin MDD, wanda ya tanaji baiwa fararen hula kariya daga yake-yake, wanda karkashin sa, MDDr ta aiwatar da tsare-tsare da dama, ciki hadda shirya ayyukan wanzar da zaman lafiya a sassa masu fama da tashe-tashen hankula da dama. (Saminu)