Tawagar kawo zaman lafiya ta MDD dake kasar jamhuriyar demokaradiyar Congo DRC (MONUSCO) ta bayyana a ranar Alhamis cewa, za ta dauki matakin kiyaye tsaron lafiyar fararen hula dake jihar Arewacin Kivu, a yayin da musanyar wuta tsakanin 'yan tawayen M23 da rundunar sojojin kasar DRC yake cigaba da ta'azara. Manzon musamman na sakatare janar na MDD a jamhuriyar demokaradiyar Congo kuma shugaban tawagar MONUSCO, Martin Kobler ya ba da umurnin kare fararen hula a wannan kasa, a cikin wata sanarwar MDD.
MONUSCO ta tabbatar da cewa, musanyar wuta ta sake barkewa a ranar Laraba 21 ga watan Agusta, tsakanin sojojin DRC-Congo da dakarun 'yan tawayen M23 a yankin Kibati mai tazarar kilomita 15 daga arewacin birnin Goma. Yankunan da aka fi samun jama'a da sansanonin sojojin MDD wadannan hare hare da makaman roka suka shafa kai tsaye. 'Na dauki niyyar ba da umurni ga sojojin tagawar MONUSCO da su mayar da martani tare da daukar matakan da suka wajaba domin kare fararen hula da kuma hana duk wata mamaya ta 'yan tawayen M23.' in ji mista Kobler. (Maman Ada)