Ofishin kula da 'yan gudun hijira na MDD a jiya Alhamis ya bukuci mahukunta a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR da su dauki mataki cikin gaggawa don kare fararen hula daga cikin rikicin siyasa da ya kunno kai wanda yanzu haka ya tilasta ma dubban al'ummomi tserewa daga gidajensu a Bangui, babban birnin kasar, in ji wani jami'i a ofishin kakakin Majalissar.
Kakakin Farhan Haq ya yi bayani ma manema labarai cewa, a cikin kwanaki 10 da suka gabata, yawan kame ta ko'ina, tsare mutane tare da azabtar da su, kwace da karfin tuwo, fashi da makami, cin zarafin, sannan da hana walwalar jama'a, kwasar ganima da kai hari a kan fararen hula ya sa mutane tserewa daga gidajensu.
Ya yi bayanin cewa, ya zuwa safiyar ranar Alhamis din nan kadai, an kiyasta akalla mutane 5,000 zuwa 6,000 ne wadanda suka hada da mata da yara kanana suka nemi mafaka a filin saukar jiragen sama na Bangui, abin da ya sa aka toshe hanyar saukar jiragen da kuma tilasta ma jiragen da za su sauke, dole canza zango suka sauka a kasar Kamaru.
Kasar jamhuriyar Afrika ta Tsakiya dai ta fada cikin rigingimu ne tun lokacin da kungiyar 'yan tawaye ta Seleka ta fara arangama tsakaninta da gwamnati tare da kwace mulki a watan Maris, abin da ya haifar da tashin hankali da rigingimu da yake nuna ya fi karfin sabon shugaba Micheal Djotodia, ya kuma sa mutane kusan 206,000 rabuwa da muhallinsu, wassu kuma 63,000 suka ma tsere don neman mafaka a kasashe makwabta, don haka yawan al'ummar kasar na miliyan 4.6 ya ragu sosai da kusan rabi wanda yawancinsu yara ne kanana, a cewar ofishin kula da 'yan gudun hijira na MDD. (Fatimah)