in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi Allah wadai da barkewar sabon tashin hankali a CAR
2014-02-11 10:42:04 cri

Wakilin musamman na babban magatakardar MDD, kuma jagoran ofishin bunkasa zaman lafiya, na kwamitin tsaron majalissar a janhuriyar Afirka ta Tsakiya CAR Janar Babacar Gaye, ya yi tir da barkewar tashin hankalin baya bayan nan a Bangui, babban birnin Afirka ta Tsakiyar. Tashin hankalin da ya yi sanadiyar kisan mutane da dama, ciki hadda Jean-Emmanuel Ndjaroua, mamba a majalissar rikon kwaryar kasar, wanda wasu 'yan bindiga suka hallaka.

Mai magana da yawun MDDr Martin Nesirky ne dai ya rawaito kalaman Janar Gaye, yayin taron manema labaru na rana rana da yake shiryawa. Ya ce, Gaye ya bayyana matukar bacin ransa, game da dauki-ba-dadi da aka kwashe makwanni ana gudanarwa a kasar, yana mai fatan mahukuntan Afirka ta Tsakiyar za su tabbatar da hukunta masu hannu cikin rura wutar rikicin.

Gaye ya kara da cewa, kwamitin tsaron MDD na jaddada kira ga daukacin masu dauke da makamai, da su ajiye makaman nasu ba tare da wani bata lokaci ba.

A wani ci gaban kuma, kakakin MDDr ya bayyana aniyar babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon, da mataimakinsa Jan Eliasson, ta ganin an shawo kan mawuyacin halin da Afirka ta Tsakiyar ta fada.

An dai dorawa rundunar BINUCA ta MDDr alhakin tabbatar da maido da doka da oda, tare da aiwatar da yarjejeniyar birnin Libreville ta shekarar bara, matakin da ya haifar da tsagaita wuta na 'dan wani lokaci, tare da kafuwar gwamnatin rikon kwarya, mai kunshe da wakilan 'yan adawar kasar da dama. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China