Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq, ya shaidawa taron manema labarai cewa, hukumomin MDD na ci gaba da taimakawa mutanen da rikicin kasar jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR) ya daidaita, ko da ya ke an fuskanci tafiyar hawainiya yayin gudanar da aikin sakamakon matsalar tsaro.
Ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD (OCHA) ya bayyana cewa, mutane kimamin 838,000 ne suka bar gidajensu a kasar, ciki har da mutane 413,000 a Bangui, babban birnin kasar. An kuma kaiwa ma'aikatan bayar da agaji hari a ranar 28 ga watan Janairu, tare da wawushe kayayyakin kungiyoyin da ba na gwamnati da ke aiki a kasar.
Bayanai na nuna cewa, hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) ta samar da abinci ga mutane kimanin 280,700 a watan Janairu, inda aka samu karuwar kashi 9 cikin 100 na wadanda suka amfana da kuma karuwar kashi 4 cikin 100 na yawan tan din abincin da aka samar a watan Disamba.
A halin da ake ciki, an samu nasarar yiwa yara 140,000 cikin yara 150,000 da ake son yiwa allurar riga-kafin cutar kyanda a sansanoni 70 da mutanen da suka rasa gidajensu ke zaune a Bangui, babban birnin kasar a farkon wannan shekara.
Fadan da ya barke a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a shekarar da ta gabata tsakanin kungiyoyin 'yan tawaye guda biyu, ya yi sanadiyar wargaza sama da mutane 825,000. (Ibrahim)