in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen Sin da Rasha na tattaunawa kan dangantaka tsakanin kasashen biyu
2014-02-07 16:52:22 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana ta kwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin a ranar Alhamis domin tattaunawa kan dangantakar dake tsakanin kasanshen biyu.

A yayin dake bayyana jin dadinsa na halartar bikin bude wasan Olympic na bazara karo na 22, mista Xi Jinping ya jaddada muhimmancin wasannin Olympic na Sochi da kuma sallar bazara ta kasar Sin.

Ganin Sochi ta karbi wadannan wasannin motsa jiki na kasa da kasa na nuna cewa kasar Rasha tana kan hanyar samun ci gaba a karkashin jagorancin shugaban kasar Vladimir Putin, in ji shugaba Xi Jinping.

Tare da nuna cewa kasashen Sin da Rasha makwabtan juna ne, abokan juna ne kuma abokan hulda ne, mista Xi ya bayyana cewa ya zo Rasha domin gabatar da jabawarsa da kansa, kamar yadda Sinawa suka saba a yayin manyan bukukuwan jin dadi a wajen makwabta.

A nasa bangare, mista Putin ya karbi mista Xi cikin fara'a tare da nuna godiyarsa kan zuwan Xi Jinping a Sochi domin taya al'ummar Rasha murnar wannan muhimmin lokaci.

Ganin cewa sallar bazara wani muhimmin lokaci ga Sinawa da su kai ziyara ga iyayensu da 'yan uwa, mista Putin ya bayyana cewa rangadin Xi Jinping a kasar Rasha wani abin alfahari ne na saduwa da babban aboki.

Haka kuma shugaban Rasha ya yi wa takwaransa na kasar Sin barka da sabauwar shekarar gargajiya ta kasar Sin da kuma yi wa 'yan wasan kasar Sin fatan samun lambobin yabo a tsawon wadannan wasannin Olympic na Sochi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China