Kakakin MDD ya bayyana cewa, a karon farko majalisar ta fadada shirinta na samar da agaji ga mazauna garin Malakal dake Sudan ta Kudu, da suka arce wa fadan da ke faruwa tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan adawa.
Farhan Haq ya bayyana a yayin taron manema labarai cewa, hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR), ta fara raba muhimman kayayyakin da jama'a ke bukata a wannan mako ga wadanda suka rasa gidajensu kimanin 10,000, a ciki da wajen Malakal. Ya ce, wannan shi ne kayan agaji na farko da aka raba wa mutanen da suka rasa gidajensu da ke zaune a wajen sansanin MDD da ke Malakal.
Alkaluma na nuna cewa, kimanin mutane 153,000 ne ke zaune a sansanin na Malakal mai nisan kilomita 600 arewa da Juba, babban birnin kasar Sudan ta Kudu da ke cikin jihar Upper Nile mai arzikin man fetur.
Kakakin na MDD ya ce, matsalar tsaro da karuwar wawushe kayayyakin agaji, sun sa har yanzu hukumomi ba sa iya kai kayan agaji zuwa wajen sansanin MDD dake Malakal, aikin da aka fara tun ranar Talata.
Kayayyakin agajin dai sun hada da jarkoki, gidan sauro, kayan girki, tabarmai, barguna da robobi wadanda aka yi jigilar su ta jirgin sama zuwa filin saukar jiragen sama da ke Malakal daga runbun adana kayayyakin hukumar na shiyya da ke Nairobi, babban birnin kasar Kenya. (Ibrahim)