Rikicin dake gudana a kasar Sudan ta Kudu ya tilastawa mutane fiye dubu 200 kaura daga gidajnesu, in ji kakakin MDD.
Hukumar daidaita harkokin jin kai ta nuna cewa, kimanin mutane dubu 201 suka kaura daga gidanjensu zuwa wasu yankunan kasar, dalilin rikicin dake ta'azzara yanzu haka a Sudan ta Kudu tun ranar 15 ga watan Disamban bara, in ji mataimakin kakakin MDD Farhan Haq a gaban manema labaru.
Kusan mutane dubu 85, aka tsugunar a Mingkaman da kuma yankunan dake kewaye da garin Awerial dake cikin jihar Lakes, in ji mista Haq.
A cewar hukumar, abinci, matsuguni, ruwan sha, kiwon lafiya su ne muhimman abubuwa domin amsa bukatun jin kai, wanda kuma samar da haka ya kan yi wahala dalilin tashe-tashen hankali, da hare-hare kan ma'aikatan ba da taimakon jin kai, ko kan kadarorinsu, kutse kan ayyukan ba da agaji da wasu kalubaloli.
Jigilar kayayyakin jin kai zuwa Bor, hedkwatar jihar Jonglei ya samu tsaiko sosai dalilin bata kashin da ake a yankin, in ji mista Haq.
Jami'in ya bayyana cewa, cibiyoyin ba da tallafin jin kai na cigaba da mai da hankali kan bangarorin dake gaba da juna domin samar da kariya ga fararen hula dake cikin bukata.
Rikicin na kasar Sudan ta Kudu ya barke a ranar 15 ga watan Disamba a yayin da gwamnatin shugaba Salva Kiir ta sanar da cewa, sojojin dake goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar da aka sauke daga mukaminsa a cikin watan Junin shakarar bara sun yi junkurin juyin mulki.
Kwamitin tsaro na MDD ya cimma wani kudurin tura sojojin 5500 da 'yan sanda 440 a makon da ya gabata domin kara karfafa karfin tawagar MDD dake Sudan ta Kudu bisa kokarin da take na kare fararen hula. (Maman Ada)